1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Arewa

Kim Jong Un ya jagoranci atisayen sojin sama

March 16, 2024

Koriya ta Arewa ta gudanar da atisayen sojin sama karkashin shugaban kasar Kim Jong Un a matsayin martani ga atisayen sojoji na hadin gwiwa da Amurka da Koriya ta Kudu suka yi a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4dnSA
Kim Jong Un
Hoto: Uncredited/KCNA/KNS/dpa/picture alliance

Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya jagoranci kasaitaccen atisayen sojin sama da aka shiya da nufin gwajin kwazon sojojin kasar na mayaye wani yanki na abokan gaba ba tare da bata lokaci ba kamar yadda kamfanin dillanci labaran gwamnati na KCNA ya ruwaito.

Wannan atisaye na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da Amurka da kawarta Koriya ta Kudu suka gudanar da nasu atisayen sojin na hadin gwiwa, lamarin da mahukutan Pyongyang ke kallo a matsayin barazana.

Karin bayani: Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka da kuma Koriya ta Kudu

Kamfanin dillancin labarai mallakar gwamnatin Koriya ta Arewa ya ce shugaban Kim Jong Un ya nuna matukar gamsuwa yayin da sojojinsa suka nuna dabaru iri-iri na yin martani cikin hamzari don murkushe abokin gaba idan ya kawo musu harin ba zata.

Tun a farkon wannan shekara dai alaka ke kara yin tsami tsakanin Koriya ta Arewa da makwabciyarta Koriya ta Kudu da ta bayyana a matsayin babbar makiyarta, tare da ficewa daga cikin dukannin hukumomin da aka kafa domin dinke baraka a tsakanin kasashen biyu.