Rasha ta soke hutun sabuwar shekara | Labarai | DW | 25.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta soke hutun sabuwar shekara

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce gwamnatinsa ta soke hutun sabuwar shekara da ministoci da wasu ma'aikata suka saba yi saboda matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

A wani sako da ya aikewa al'ummar kasar ta gidajen talabijin, Shugaba Putin ya ce ministocin nasa da sauran wanda wannan abu ya shafa za su cigaba da yin aiki ne kamar yadda suka saba ba tare da sun tafi hutu ba.

Bisa al'ada dai a kasar ta Rasha wani bangare na ma'aikata da ministoci kan gudanar da hutu ne daga 1 ga watan Janairu zuwa 12 gawata don yin shagugulan shiga sabuwar shekara.