Rasha ta rufe ofishin Amnesty International a birnin Mosko | Labarai | DW | 02.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta rufe ofishin Amnesty International a birnin Mosko

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Laraba, kungiyar ta Amnesty International ta sanar cewa an rufe mata ofishinta da ke birnin na Mosko ba tare da wani bayani ba.

Ma'aikatan wannan ofishi na birnin Mosko sun ce da safiyar wannan Laraba ce suka fuskanci hakan bayan da suka ga shaidar rufe ofishin na su a cewar wata sanarwa ta kungiyar ta Amnesty International.

Ta shafinsa na Facebook Ivan Kondratenko daya daga cikin ma'aikatan kungiyar ta Amnesty reshen kasar Rasha ya ce dukannin kayayyakin aikinsu na nan cikin ofishin, amma kuma yana garkame. Daga nata bangare kungiyar ta Amnesty International ta saka hoton tambarin da ke nuni da cewa an rufe musu wannan ma'aikata ta birnin Mosko, inda suke aiki tun yau da shekaru 20.

Kakakin fadar shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP ya tuntuba, ya ce ba shi da wata masaniya kan wannan batu, inda ya ce shi ma ya ji ana fadi.