Rasha ta musanta hannu a rikicin kasar Siriya | Labarai | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta musanta hannu a rikicin kasar Siriya

Wata jaridar birnin Mosko ta rawaito majiyoyin sojin Rasha na cewa fadar Kremlin ta aike da makaman yaki ga gwamnatin Siriya.

Syrien Sergej Lawrow und Bashar Assad in Damaskus

Sergei Lavrov da Bashar Assad a birnin Damaskus

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce kasarsa ba ta dauki karin matakan karfafa sojojinta a Siriya ba. Lavrov ya fada wa 'yan jarida a birnin Mosko cewa kwararrun sojojin Rasha sun kwashe shekaru da yawa suna aiki a Siriya musamman horas da sojojin kasar, wanda ya ce hakan ba wani sirii ba ne. Ya ce har yanzu fadar Kremlin babbar kawa ce ga shugaban Siriya Bashar al-Assad. Da farko dai wata jaridar birnin Mosko ta rawaito cewa Rasha na kan tura makaman yaki zuwa Siriya. Sannan Amirka ta ce tana da kwakkwarar shaidar cewa Rasha na da hannu dumu-dumu a rikicin na Siriya.