1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kwace iko da Bogdanivka na Ukraine

April 21, 2024

Rasha ta kwace iko da garin ta Bogdanivka ne a daidai lokacin da Ukraine ke murnar samun tallafin dala biliyan 61 daga Amirka.

https://p.dw.com/p/4f1om
Dakarun Ukraine a Chasiv Yar
Dakarun Ukraine a Chasiv YarHoto: Narciso Contreras/Anadolu Agency/picture alliance

Rasha ta ce ta samu iko a kusa da filin daga da ke garin Chasiv Yar na gabashin Ukraine. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Ukraine din ke shirin karbar tallafin yaki na dala biliyan 61 daga Amirka. Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce ta kwace iko da garin Bogdanivka kilo mita uku zuwa arewa maso gabashin Chasiv Yar.

Karin bayani:Yunkurin Rasha na kwace wani yankin Ukraine ya haifar da fargaba

Garin da ke da yawan al'umma 13,000 gabanin fara yakin ya zama tamkar kufai a yanzu sakamakon tserewa rikici da mutane suka yi.

A farkon wannan watan na Afrilu ne, dakarun Kyiv suka ce fada ya kara rincabewa a fagen daga da ke Chasiv Yar inda Rasha ke luguden wuta ba kaukkautawa, lamarin da ya haifar da karuwar asarar rayukan fararen hula.