1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kaddamar da hari kan Donbass

Abdourahamane Hassane MAB
April 19, 2022

Rasha ta kaddamar da gagarumin farmaki a gabashin Ukraine a yankin Donbass, kwanaki kadan bayan da sojojinta suka janye daga kewayen birnin Kiev.

https://p.dw.com/p/4A6pR
Ukraine Rubischne | Einschussloch in Fenster | TASS-Bild
Hoto: Stanislav Krasilnikov/Tass/picture alliance

Sojojin saman Rasha sun yi amfani da makamai masu linzami da tankokin yaki wajen tarwatsa wasu sananonin sojin 13 a Donbass. A halin da ake ciki hukumomin Ukraine sun yi kira ga mazauna yankin da su gudu su tsira da rayukansu, duk da cewar babu hanyoyin jin kai na ficewa.

Rasha ta yi kira ga daukacin sojojin Ukraine da su ajiye makamansu domin mika wuya. Donbass wanda wani bangarenta ke karkashin ikon 'yan aware masu goyon bayan Rashar tun shekara ta 2014. Zai kasance wani sabon fagen daga a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.