1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta mamaye Ukraine ta sama da kasa

Abdullahi Tanko Bala
February 24, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce a shirye ta ke ta karbi 'yan gudun hijira da ke guje wa mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine yayin da a waje guda kasashen yamma ke kakaba sabbin takunkumi a kan Rasha

https://p.dw.com/p/47Xob
Ukraine | Zerstörtes Militärgerät bei Mariupol
Hoto: Sergei Grits/AP Photo/picture alliance

Babban jami'in harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Joseph Borell ya aike da sammaci ga jakadan Rasha a kungiyar EU Vladimir Chizhov, ya baiyana a hedikwatar tarayyar Turan a Brussels.

Kungiyar ta EU ta yi kakkausar suka tare da yin tir da mamayar Ukraine da Rashar ta yi babu gaira babu dalili a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun EU kan manufofin harkokin waje Peter Stano ya fitar.

Ku ta bukaci Putin ya gaggauta kawo karshen farmakin sannan ya janye sojojinsa da kuma makamai daga yankin Ukraine.

Jamus da EU da kungiyar kawancen tsaro ta NATO duk sun yi Allah wadarai da Rasha kan harin.