Rasha ta kaddamar da hare-hare a birnin Kyiv na Ukraine
November 14, 2025
Talla
Hukumomi a Ukraine sun ce harin na Rasha ya yi wa gine-gine da dama illa, tare da haifar da fashe-fashe da gobara a wasu sassa na birnin Kyiv fadar gwamnatin kasar.
Magajin garin birnin, Vitali Klitschko, ya tabbatar da cewa mutane biyu sun ji rauni a cikin hare-haren na yau.
A cikin sakon da ya wallafa a shafin Telegram, Klitschko ya bayyana cewa birnin Kyiv na karkashin hare-haren Rasha, tare da umartar mazauna da su garzaya wuraren buya domin tsira.
Shugaban hukumar kula da tsaron rundunar soja ta Kyiv, Tymur Tkachenko, ya bayar da umarni ga rundunonin agajin gaggawa da su yi hanzarin zuwa yankunan da abin ya shafa domin tunkarar illolin harin.