1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta saka takunkumi ga 'yan Ukraine

Gazali Abdou Tasawa
November 1, 2018

Kasar Rasha ta dauki matakin haramta wa wasu manyan 'yan siyasa 322 da kuma kamfanoni 68 na kasar Ukraine taba kudaden ajiyar bankinsu a Rasha a matsayin martanin ga kuntata wa 'yan Rasha a Ukraine.

https://p.dw.com/p/37W6m
Portraitfoto: Wladimir Wladimirowitsch Putin
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Kasar Rasha ta dauki matakin ladabtarwa na tattalin arziki kan wasu manyan 'yan siyasa 322 da kuma kamfanoni 68 na kasar Ukraine a matsayin martani ga abin da ta kira kuntatawar da mahukuntan kasar ta ukraine suke yi wa wasu kamfanoni da jama'a na kasar ta Rasha mazauna kasar ta Ukraine.

Matakin wanda ya tanadi hana wa Ukrainiyawan taba kudaden ajiyarsu na banki a kasar ta Rasha ko kuma fitar da kudade daga kasar zuwa kasarsu ta Ukraine, zai shafi babban dan shugaban kasa ta Ukraine Petro Porochenko da tsaffin firamnistan kasar guda biyu Arseni Latseniouk da Loulia Timochtchenko kazalika da alkalai da 'yan majalisar dokoki da wasu attajiran kasar ta Ukraine. 

Dangantaka tsakanin Rasha da Ukraine dai ta tabarbare ne daga shekara ta 2014 tun bayan hawan mulki Shugaba Porochanko mai samun goyon bayan kasashen Turai da kuma mamayar da rasha ta yi wa yankin Krimiya na kasar ta Ukraine.