Rasha ta dakatar da zirga-zirgar jirage tsakaninta da Masar | Labarai | DW | 06.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta dakatar da zirga-zirgar jirage tsakaninta da Masar

Dmitry Peskov da ke magana da yawun shugaba Vladimir Putin ya cewannan dakatarwa ta shafi dukkanin jirage ne da ke zirga-zirga tsakanin kasashen biyu.

Putin Portrait Symbolbild NGO-Agenten-Gesetz Russland

Shugaba Putin na Rasha

Kasar Rasha ta tsaida duk wata zirga-zirgar jiragen sama tsakanin birnin Moscowa zuwa Alkhahirar Masar har sai masu aikin bincike sun gano musabbabin hadarin da ya jawo tarwatsewar jirgin kasar a samaniya a makon da ya gabata.

Mahukuntan na fadar Kremlin sun bayyana haka ne a ranar Juma'an nan inda a cewar Dmitry Peskov da ke magana da yawun shugaba Vladimir Putin wannan batu ya shafi dukkanin jirage ne.

Mista Peskov ya fada wa manema labarai cewa shugaba Putin ya dauki wannan mataki ne bayan da ya ji ta bakin kwamatin yaki da ayyukan ta'addanci na kasar ta Rasha.

Shi ma Alexander Bortnikov shugaban sashin tsaro na kasar ta Rasha ya ce babu wani dalili na ci gaba da zirga-zirgar jiragen har sai an tabbatar da dalilan hadarin jirgin kasar ta Rasha da ya yi hadari a yankin Sinai na kasar ta Masar, abin da ya yi sanadin rayukan mutane 224.