Rasha ta ce Ukraine ke kafar ungulu a yarjejeniyar Minsk | Labarai | DW | 26.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ce Ukraine ke kafar ungulu a yarjejeniyar Minsk

A cewar kasar ta Rasha a shirye take ta karfafa dangantaka da Turai da Amirka muddin ba a yi mata shishshigi.

Russland Sergej Lawrow PK zur Außenpolitik

Sergey Lavrov

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa kasar Ukraine kejan kafa a shirin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla ta Minsk saboda tana fatan ganin ci gaba da kasancewar takunkumin karya tattalin arziki da kassahen yamma suka kakabawa kasar ta Rasha.

Sergey Lavrov ya bayyana haka ne a ranar Talatan nan a wani taron manema labarai inda ya ce kasar ta Ukraine na rabewa da kasashen na Yamma ba ta son daukar na ta nauyin cikin yarjejeniyar da suka cimma.

Mista Lavrov ya kuma kara da cewa: "A shirye muke dan samar da hadin kai mai karfi da 'yan uwanmu a Yammacin duniya ciki kuwa har da kasashen Turai da Amirka, kofarmu a bude take danm samun ci gaba da hadin kai muddin dai wata kasa ba ta so tza yi mana shishshiga ba a harkokinmu na cikin gida wanda muma ba zamu yi musu ba dole a mutunta juna".