1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na zargin Ukraine da yi mata zagon kasa

June 6, 2023

Fadar Kremlin ta zargi Ukraine da yi mata zagon kasa, tare da ikirarin cewa Kyiv ce ke da alhakain kai harin da ya tarwatsa madatsar ruwan Kakhovka da ke kudancin Ukraine.

https://p.dw.com/p/4SGIR
Hoto: SERGIY DOLLAR/AFP/Getty Images

Kakakin gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya ce abin da Ukraine ta yi a nuna karara cewa an shirya tare da kai harin ne da gan-gan saboda wata manufa.

Sai dai kuma gwamnatin kasar Ukraine da sauran kasashen yammacin Turai na zargin kasar Rasha ne da kai hari kan madatsar ruwan Kakhovka a safiyar wannan Talata, domin kawo tsaiko ga shirin Ukraine da ma aikata wani abu ma kama da ramuwar gayya.

Tuni dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya bukaci kwamittin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan ya gudanar da taron gaggawa sakamakon wannan harin.

Rasha dai ta sanya dokar ta-baci a yankin da madatsar ruwan ta tarwatse sakamakon ambaliyar ruwa da ya faru a can.