Rasha na kara girke dakaru a Ukraine | Labarai | DW | 19.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na kara girke dakaru a Ukraine

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta ce har yanzu akwai dubban dakarun Rasha a kan iyakar kasar da gabashin Ukraine.

Babban sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya ce akwai dubban dakarun Rasha a kan iyakar gabashin Ukraine, a wani abin da ya kira girke dakaru da ke mayar da hannun agogo baya. Ya ce yanzu haka ana ganin yadda Rasha ke sake tura dakarunta a kan iyakar Ukraine. Ya ce wannan matakin da Rasha ke dauka na zama wani sabon yunkuri na yin katsalanda a Ukraine. Saboda haka ya ce dole gamaiyar kasa da kasa ta mayar da martani mai karfi idan Rasha ta zabi yin katsalanda a Ukraine din.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu