Rasha na ikirarin nasara a Siriya | Labarai | DW | 03.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha na ikirarin nasara a Siriya

Duk da wannan ikirari da Rashar ke yi Amirka na zarginta da marawa Assad baya duk da cewa shi ake dorawa alhakin halin da Siriyar ke ciki.

Bisa bayanan da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar, Rasha na zargin cewa hare-haren da ta ke kaiwa ta sama domin murkushe mayakan kungiyar IS a Siriya, ya tilastawa wasu 'yan tawaye su kusan 600 barin kasar zuwa Turai.

A yayin da yake bitan kwanaki ukun da Rashar ta yi tana luguden wuta ta sama a Siriyar, daya daga cikin manyan hafsoshin sojin kasar ya ce sun kai hari kan matattara 50, kuma za su cigaba da inganta hare-haren na su.

Hafsan sojin ya ce bacin haka kuma, sun yi nasarar lalata wuraren ajiyan makaman, 'yan wannan kungiya, da tashoshin sadarwarsu da wuraren da suke atisaye, da ma wuraren da ake hada makaman da masu kunar bakin wake ke amfani da su.Wannan hari na Rasha dai na cigaba da shan suka a al'ummar kasa da kasa musamman Amirka wadda ke zarginta da kai harin kan duk wanda ke adawa shugaba Bashar al-Assad, duk da zargin cewa, dakarun shi ne suka fi kowani bangare yin ta'adi, musamman wajen kai hari kan fararen hula.