1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha na ci gaba da kai hare-hare a Ukraine

Mouhamadou Awal Balarabe
March 1, 2022

Sojojin Ukraine na fuskantar sabon farmakin daga dakarun Rasha a biranen Kiev da Kharkiv da wasu garuruwa, kwana guda bayan tattaunawar farko da ba ta yi nasara ba.

https://p.dw.com/p/47mV0
Ukraine | Zerstörung in Charkiw
Hoto: State service of special communication and information protection of Ukraine/AP/picture alliance

A wannan rana ta shida ta mamaya, Rasha ta yi ruwan bama-bamai a tsakiyar Kharkiv, birni na biyu mafi girma a kasar Ukraine, a daidai lokacin da kasashen yammacin duniya ke kara kakaba mata takunkumi.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta Ukraine ta fitar, ta bayyana cewa Rasha ta tura motocin sulke, da makamai atilari domin yin mata kawanya da nufin mayar da biranen Kiev da Kharkiv da Odessa da Kherson da Mariupol karkashin ikonsu.

Gwamnan yankin Donetsk ya nunar da cewa an katse wutar lantarki a babban tashar jiragen ruwa na Mariupol da ke Kudu maso gabashin Ukraine. kasar dai ta bayar da rahoton mutuwar fararen hula 352 yayin da wasu 2,040 suka jikkata tun bayan mamayar, sannan ta ce dubban sojojin Rasha sun halaka.