Rasha da Ukraine suna dinke barakar da ke tsakani | Labarai | DW | 18.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha da Ukraine suna dinke barakar da ke tsakani

Kasashen Rasha da Ukraine sun amince da yarjejeniya kan iskar gas

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Ukraine Petro Poroshenko sun amince da yarjejeniyar da Rasha za ta koma samar da isakar gas wa Ukraine.

Bangarorin biyu sun gana yayin taro tsakanin kasashen Asiya da Turai da ya gudana a birnin Milan na kasar Italiya, kuma Shugaba Putin na Rasha ya bayyana amincewar, inda ya ce za a samar da iskar gas wa Ukraine lokacin sanyin hunturu, kuma bangarorin biyu za su ci gaba da ganawa a mako mai zuwa, a birnin Brussels na kasar Beljiyam. Sai dai duk da wannan ci gaba Firaministan kasar Italiya mai masaukin bakin taron Matteo Renzi ya ce akwai wagegen gibi tsakanin bangarorin biyu na Rasha da Ukraine.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman