Rasha da Turkiyya za su yi aiki tare
December 29, 2020Talla
Kasashen na Rasha da Turkiyya sun jaddada matsayarsu ta aiki kafa da kafa da juna a wurin ganawar da ministocin harkokin wajensu suka yi a a wannan Talata.
"Dangantakar tsakanin Turkiyya da Rasha za ta ci gaba ba tare da dogaro a kan kowa ba, ba ma bukatar agajin 'yan hamayya na kasashen yamma.'' inji Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov.
Ministan harkokin wajen na Rasha ya kuma ce da su da Turkiyya za su ci gaba da daukar matsaya mai kyau a siyasar duniya domin cimma muradun kasashensu.