1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rage amfani da makamashin da ba a sabuntawa

December 13, 2023

Kasashe a taron Majalisar Dinkin Dunjiya kan sauyin yanayi COP28 sun amince da rage amfani da makamashin da ba a sabuintawa daga nan zuwa shekarar 2050

https://p.dw.com/p/4a7t2
Vereinigte Arabische Emirate | COP 28 Klimakonferenz Dubai
Hoto: Amr Alfiky/REUTERS

Bayan gomman shekaru ana tattaunawa, kasashen duniya sun cimma gagarumar yarjejeniya inda suka yi kiran janyewa sannu a hankali daga amfani da makamashin da ba a sabuntawa, ko da yake taron bai yanke karara cewa za a daina amfani da makamashin wanda ya hada da kwal da man fetur da kuma gas ba.

Karin Bayani: Dubai: Yunkurin kasashen duniya na rage dumamar yanayi

COP28 | Sultan al-Dschaber
Hoto: Kamran Jebreili/AP/dpa/picture alliance

Kasar Hadaddiyar daular Larabawa wadda ta karbi bakuncin taron ita ce ta gabatar da kundin yarjejeniyar wanda kasashe kimanin 200 da suka halarci taron suka amince.


Masana kimiyya sun yi ammanar cewa makamashin kwal da fetur da kuma gas suna taimakawa wajen fidda gurbatacciyar iska ko hayaki da ke gurbata muhalli.

Mahalarta taron sauyin yanayi na duniya COP 28 a Dubai
Hoto: Kamran Jebreili/AP Photo/picture alliance

Wannan dai shi ne karon farko da aka cimma irin wannan yarjejeniya cikin shekaru da dama a tarihin tarukan muhalli na Majalisar Dinkin Duniya.

Masana dai na ganin har yanzu da sauran rina a kaba wajen cimma kudirin kare dumamar duniya da kuma illar da hakan ke haifarwa a cewar Dr Auwal Faruk Abdulsalam shugaban tsangayar nazarin Muhalli ta jami'ar jahar Kaduna a Najeriya.