Ra′ayoyi mabambanta kan nukiliyar Iran | Siyasa | DW | 03.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ra'ayoyi mabambanta kan nukiliyar Iran

Ana ci gaba da mayar da martani kan wata matsaya da aka cimma tsakanin manyan kasashen duniya da Iran,da ake fata za ta kai ga samar da yarjejeniya dauwamammiya.

Atomverhandlungen zwischen US-Außenminister John Kerry und iranischem Außenminister Javad Zarif im schweizerischen Lausanne

Wakilan kasashe a taron Lausanne a kasar Switzerland

Kimanin shekaru 12 aka kwashe ana tattaunawa kan shirin nukiliyar ta Iran, da kasar ta ce na samar da makamashi ne amma ake zarginta da kokarin kera makaman nukiliya.

Kwarya-kwaryar yarjejeniyar da aka cimma da Iran na zama wani albishir ga yankin Gabas ta Tsakiya da ma gamaiyar kasa da kasa. Sai dai ba a sani ba ko za ta kai ga warware takaddamar shirin nukiliyar na Iran. 'Yan kasar dai sun kwashe tsawon dare har zuwa wayewar gari ranar Jumma'a suna bukukuwan cimma yarjejeniyar da shugaban Amirka Barack Obama ya ce wani abu ne na tarihi amma ya ce da jan aiki gaba kuma za a ci gaba da sa ido kan take-taken Iran.

"Ko shakka babu wannan shirin kadai ko da an aiwatar da shi dari bisa dari ba zai kawo karshen bambamci da rashin yarda da ke tsakanin kasashenmu biyu ba. Har gobe damuwarmu game da Iran shi ne yadda ta ke tallafa wa ayyukan ta'addanci da haddasa hargitsi a yankin Gabas ta Tsakiya da barazanar da take wa kawayenmu irinsu Isra'ila."

Daukacin kasahen yankin dai sun yi maraba da matsayar da aka cimma. Sarkin Saudiya Salman ya shaida wa Shugaban Amirka Barack Obama cewa yana fata yarjejeniyar karshe da za a kulla za ta tabbatar da zaman lafiya a yankin da duniya baki daya.

Lausanne Atomverhandlungen Abschlußstatement Steinmeier Mogherini Javad Zarif

Walter Steinmeier Federica Mogherini Javad Zarif

Babbar jami'ar kula da harkokin ketare na tarayyar Turai wadda ta jagoranci tawagar kasashen yamma a taron na Lausanne a kasar Switzerland Federica Mogherini ta yaba da ci-gaban da aka samu.

A martanin da ya mayar ministan harkokin wajen Jamus da ke zama cikin manyan jami'an diplomasiyya da suka shiga tattaunawar baya-bayan nan ta tsawon kwanaki a kasar Switzerland, Frank-Walter Steinmeier ya bayyana yarjejeniyar da wani gagarumin ci gaba a kan turba da ta dace.

"Ko shakka babu babban ci gaba ne. An yi ta fadi tashi kafin a kawar da abubuwan da suka yi ta hana ruwa gudu tsawon shekaru 12. Sabili da haka na yi amanna a matakin farko an gamsu da wannan matsayar."

Sai dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda tun farko ya so duniya ta dauki matakan ba sani ba sabo kan Iran, a wannan Juma'a ya ce an samu hadin kai da shi da majalisar ministocinsa wajen nuna adawa da wannan yarjejeniya da aka cimma da Iran.

"Kan majalisar zartaswa ya hadu na yin tir da wannan shiri. Domin wannan shirin babban hatsari ne ga yankin da ma duniya wanda kuwa zai yi bazarana ga wanzuwar kasar Isra'ila. Saboda haka Isra'ila ba za ta amince da wata yarjejeniya da za ta ba wa wata kasa da ta sha alwashin kawar da Isra'ila damar kera makaman nukiliya ba."

Yanzu haka dai kasar Iran da kasashe shida masu fada a ji a duniya da suka amince da wannan matsaya kan shirin nukiliyar hukumomin birnin Teheran, sun ba wa kansu wa'adin zuwa ranar 30 ga watan Yuni na cimma yarjejeniyar karshe.

Sauti da bidiyo akan labarin