Putin ya gode wa Amirka kan kungiyar IS | Labarai | DW | 17.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin ya gode wa Amirka kan kungiyar IS

Shugaba Putin na Rasha ya gode wa Shugaba Trump kan bayanan CIA na yunkurin Kungiyar IS na kai hari a birnin Saint-Petersbourg.

Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya gabatar da godiyarsa ga takwaransa na Amirka Donald Trump dangane da bayanan da hukumar leken asirin Amirka ta CIA ta bai wa kasarsar ta Rasha da kuma suka bai wa hukumar leken asirin kasar ta Rasha ta FSB damar bankado wani harin ta'addanci da Kungiyar IS  ta shirya kaiwa a birnin Saint-Petersbourg a jiya Asabar. 

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Rasha ya ruwaito cewa Shugaba Putin ya isar da godiyar tasa ce a wata fira da ya yi ta wayar tarho a wannan Lahadi da Shugaba Trump. 

A ranar Jumma'ar da ta gabata hukumar leken asirin kasar ta Rasha ta FSB ta sanar da kama wasu mutane bakwai da ke shirin kai harin ta'addanci a birnin na biyu mafi girma a kasar ta Rasha tare da karbe tarin bindigogi da ababe masu fashewa kirar gargajiya wadanda mutanen suka so yin amfani da su wajen kai harin.