Putin ya ce za a iya warware rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 18.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Putin ya ce za a iya warware rikicin nukiliyar Iran

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya shaidawa takwaransa na Iran Hassan Rouhani cewar akwai dama da ake da ita ta warware rikicin nukiliyar kasar Iran.

Rahotannin da ke fitowa daga fadar mulkin Rasha ta Kremlin da ke birnin Moscow na cewar shugaba Putin ya bawa Mr. Rouhani wannan tabbacin ne a wata zantawa da suka yi ta wayar tarho, yayin da ya rage kwanaki biyu kafin a gudanar da wani taro tsakanin Iran din da kasashen nan shidda da ke kokarin shawo kan Iran din dangane da dakatar da shirinta na nukiliya.

Baya ga wannan batu, shugabannin biyu sun kuma tattauna dangane da halin da ake ciki a Siriya inda dukanninsu suka bada goyon banyansu na kokarin da ake yi wajen gudanar da taro na kasa da kasa da nufin lalaubo hanyoyin da za bi wajen warware yakin basasar Siriyan wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balaraba