1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita kan rikicin Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar
December 22, 2022

Kusan watanni 10 bayan fara yaki da Ukraine, Shugaban Vladimir Putin na Rasha ya ba da alamun amincewa da hawa teburin tattaunawa.

https://p.dw.com/p/4LLGd
Russland l Präsident Putin, Sitzung des Vorstands des russischen Verteidigungsministeriums
Hoto: Sergei Fadeichev/TASS/dpa/picture-alliance

Hawa teburin sulhu ne kadai mafita daga cikin kowane irin rikici da ya hada da amfani da makamai, kuma Rasha ba ta taba kaucewa yin hakan ba, sabanin Ukraine, "in ji shi a wani taron manema labarai a wannan Alhamis.

Bugu da kari ya ce, mahukuntan Ukraine sun kaurace daga duk wata tattaunawa. A kan haka ne Putin ya ce da zai fi dacewa Kiev abu mai kyau, idan da fahimci cewa mafita daga wannan rikici ita ce tattaunawa.

Sabanin Kiev, Moscow na so a yi nazari kan tushen halin da ake ciki yanzu tare kuma da yin la'akari da yankunan da suka koma karkashin ikonta, da aka ce ta sabawa dokokin kasa da kasa.