1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin: Mun fi Amirka karfin makaman nukiliya

March 13, 2024

Gargadin na Shugaba Putin na zuwa ne 'yan kwanaki gabanin babban zaben kasar da za a gudanar wanda tuni aka kammala hasashen Shugaba Putin ne zai lashe zaben ba tare da wata tangarda ba.

https://p.dw.com/p/4dTNg
Hoto: Evgenia Novozhenina/REUTERS

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya jinjina wa kasar kan karfin makamin nukiliya da take da shi, yana mai gargadin cewa Rasha a shirye take ta fara amfani da wadannan makamai madamar aka taba mutuncin kasarsa.

''Mun shirya amfani da makamin nukiliya kuma makamanmu sun fi karfin na manyan kasashen duniya. Namu da na Amirka ne kawai suke daidai. Kuma mu mun yi nisa ma a inganta namu makaman masu guba a nan gida.'' in ji Shugaba Putin cikin wata hira ta musamman da aka yi da shi a kafar yada labaran Rasha

Kalaman na Shugaba Putin din na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da dakarun Ukraine suka kai wa matatun fetur na Moscow wani mummunan hari, masu sharhi kuma na ganin hakan ne ya sanya shi barazanar fara amfani da makaman nanukiliya.