EU za ta hukunta Belarus
May 24, 2021Talla
Gwamnatin kasar Poland ta nuna bukatar EU ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninta da kasar Belarus har sai an saki dan jaridar da aka kama Roman Protasevich. Kungiyar EU za ta yi nazari don cimma matsaya kan mataki na gaba don hukunta gwamnatin Belarus kan wannan mataki.
Hukumomin kasar Belarus sun tilasta jirgin fasinjan Ryanair da ya tashi daga Girka ya nufin zuwa Lithuania amma aka sauya akalar jirgin zuwa Minsk babban birnin kasar Belarus saboda dalilan na tsaro, amma daga bisani aka kama wani fitaccen dan jaridar kasar da ke cikin jirgin. Gwamnatin Belarus ta dade tana neman Roman Protasevich ruwa a jallo saboda gudanar da wata haramtacciyar kungiya.