PDP ta yi zanga-zanga kan zaben Imo | Labarai | DW | 20.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

PDP ta yi zanga-zanga kan zaben Imo

Dubban magoya bayan jamiyyar PDP da ke adawa a Najeriya sun yi zanga-zangar lumana a Abuja, inda suka nuna rashin amincewa da hukuncin kotun koli kan zaben jihar Imo da ke kudancin kasar.

Hukuncin kotun koli a da aka fidda a makon jiya dai kan zaben gwamnan jihar Imo ya bayyana cewar Hope Uzodinma na jam'iyyar PDP wanda ya zo na hudu a zaben shi ne halastaccen gwamnan jihar.

Kotun dai ta ce ta yanke wannan hukuci ne bisa la'akari da kuri'u na wasu akwatuna sama da 300 da ba a kidaya da su ba a lokacin da aka sanar da zaben gwamnan jihar wanda ya bawa jam'iyyar PDP nasara.

Shugaban jamiyyar ta PDP Uche Secondus ya ce hukluncin kotun hatsari ne ga demokurdiyyar Najeriya domin kotu ce madafa ta karshe ga duk wanda aka yi  wa ba daidai ba, amma kuma gashi kotun ta kasa share masu hawayensu.