Paparoma ya isa Turkiya | Labarai | DW | 28.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya isa Turkiya

Paparoma Benedict na 16 ya isa birnin Ankara na kasar Turkiya,ziyara ta farko zuwa kasar Musulmi inda zai nemi ya kwantar da hankula tun bayan kalamansa na batunci ga Islama tare da sasantawa da kiristoci yan Orthodox na duniya baki daya.

Paparoman ya isa Ankara ne cikin tsauraran matakan tsaro don kare duk wani kokari na kawo cikas ga wannan ziyara ta kwanaki 4 .

Duban jamaa ne dai sukayi zanga zanga na kin jinin wannan ziyara.