Asalin sunan Paparoma Francis dai shi ne Jorge Mario Bergoglio kuma an haife shi ne a shekarar 1936 a kasar Argentina.
A cikin shekarar 2013 ne ya zama Paparoma wato shugaban mabiya darikar Katolika ta duniya. Shi ne Paparoma na 266 da aka samu, kuma shi ne mutum na farko a yankin Latin Amirka da ya hau wannan matsayi.