Paparoma ya damu da kashe-kashe a Syria | Labarai | DW | 17.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya damu da kashe-kashe a Syria

A sakonsa na bikin Easter a bana, Paparoma Francis ya bayyana matukar damuwa kan irin tashin hankali da kiyayyar da yake-yake ke haddasawa a duniya.

Paparoma Francis musamman ya koka kan kisar fararen hula masu yawa na baya-bayannan a kasar Syria.

A jawaban da ya gabatar albarkacin zagayowar lokacin na Easter da mabiya addinin Kirista ke ciki a fadin duniya, Paparoman ya kuma damu da karuwar wasu matsalolin da suka shafi safarar mutane da rashawa da fari dama cin zarafin mata a wasu sassa na duniya.

Sai kuma bukatar karfafa imani, musamman a wannan lokacin da jama'a ke ga alamu baudewa kan yadda al'amura ke kara ta'azzara a sassan duniyar daban-daban.