Paparoma Francis ya yi kiran da a samar da zaman lafiya | Labarai | DW | 16.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis ya yi kiran da a samar da zaman lafiya

Paparoman ya yi kiran da a samar da zaman lafiya a Yankin Gabas ta tsakiyya da ma Siriya inda yakin da aka kwashe kusan shekaru shida ana yi, ke ci gaba da janyo asarar rayukan jama'a tare kuma da zama abin tsoro.

Faparoma Francis  wanda ya bayyana haka a lokacin adu'oin da ya yi na bukukuwan Easter a jawabin da ya yi a dandali Saint-Pierre na Urbi da Orbi a gaban mabiya kusan dubu sitin. Ya kuma ce a kasashen Yankin Gabas ta tsakiya hade da Yemen da Siriya da Iraki akwai bukatar ci gaba da yin adu'a domin tabbatar da zaman lafiya,ya ce hakan kuwa ba zai tabbata ba, sai da hadin kan shugabanni.