Paparoma Francis na shirin kai ziyarar farko a Afrika | Labarai | DW | 24.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis na shirin kai ziyarar farko a Afrika

Wannan dai shi ne karon farko da babban jami'in cocin Katholika zai ziyarci nahiyar ta Afirka tun kuma ziyar ta zo lokacin da ayyukan ta'addanci ke karuwa a duniya

Jami'an tsaron kasar Kenya dai na shirin samar da dakarun tsaro har dubu goma a biranen Kasashen Kenya da Yuganda a yayin ziyarar Paparoma Francis wacce ta kunshi ganawa da talakawa.

Biranen Nairobi da Kampala dai na fuskantar hare-haren 'yan kungiyar Al-Qaeda dake a gabashin Afrika gami da kungiyar Al-shabbab bisa martani kan shiga yakin Somaliya da kasashen suka yi.

Babban jami'in 'yan sandan Kenyan dai ya tabbatar da cewar sun kammala dukkan wasu shirye-shiryen karbar bakuncin Paparoman da zai fara a ranar Larabar nan.