Paparoma: Akwai matsala a Afirka da Yemen | Labarai | DW | 08.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma: Akwai matsala a Afirka da Yemen

Shugaban darikar Roman Katolika na duniya Paparoma Francis, ya nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin rayuwa da mutane ke fama da ita a kasashen Afirka da kuma Yemen.

Paparoma Francis da ya tabo musamman batun yawan cin zarafin da ke kasashen, yana mai jan hankalin shugabannin duniya da su sake tunani kan wadannan matsaloli da jama'a ke fuskanta.

Paparoma ya yaba taimakon manyan kasashe masu arziki ta fusknata kyautata harkokin tattalin arziki, sai da ya ce akwai bukatar a sa hankali kan Yemen da Sudan ta Kudu da kasashen yankin tafkin Chadi da Somaliya. Ya ce yaki bai taba zama maganin matsala ba a tarihin duniya.

Sama da mutane miliyan 30 ne ke fuskantar tsananin karancin abinci da sukuni a wadannan kasashen da shugaban Katolikan duniya ya lasafta.