Pakistan: Shekaru 70 da samun ′yancin kai | Labarai | DW | 14.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Pakistan: Shekaru 70 da samun 'yancin kai

A wannan Litinin al'umar kasar Pakistan ke gudanar da bikin murnar cika shekaru saba'in da samun 'yanci a wani kasaitaccen biki da aka soma tun daga daren jiya Lahadi da gagarumin wasan wuta.

Al'umar kasar Pakistan na gudanar da bikin murnar cika shekaru saba'in da samun 'yancin kai inda aka soma gudanar da kasaitaccen bikin da aka shirya tun daga daren jiya Lahadi da gagarumin wasan wuta kafin yau Litinin a dora da fareti na musanman a sansanin sojin saman kasar da ke Asghar Khan a yankin Risalpur.

 A ranar 14 ga watan Augusta na shekarar 1947 kasar ta Pakistan ta samu 'yancin kai bayan da ta balle daga kasar Indiya, A gobe Talata makwabciyar kasar, wato Indiya ke na ta bikin samun 'yancin. Kasashen biyu sun sami 'yanci ne daga turawa mulkin mallaka na Birtaniya a shekara guda .