1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korar jami'an Rasha daga Ostriya

February 2, 2023

Ostriya ta sanar da korar wasu jami'an diflomasiyya na Rasha da ke kasar wadanda ta baiyana cewa ba a bukatar su.

https://p.dw.com/p/4N1xC
Österreich | Agentur der Europäischen Union für Grundrechte (FRA) in Wien
Hoto: Google Maps

Matakin korar jami'an diflomasiyyan hudu na Rasha ciki har da guda biyu da ke wakiltar Rasha a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Vienna dai ya zo da mamaki duba da yadda kasar ta ki saka baki a yakin da Rasha ke yi a Ukraine domin kafin fara yakin Ostriyan na da kyakyawar alaka da Rashar.

A sanarwar da ma'aikartar harkokin wajen Ostriya ta fitar ta ce ta ba wa jam'ian hudu wa'adin mako guda su tattara su fice daga kasar sai dai ba ta sanar ba da wani dalili.

Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar Vienna ke korar jami'an Rasha daga kasar ba, domin ko da a watan Ogustan 2020 Ostriyar ta kori wani jami'in Rasha da ta ke zargi da leken asiri kana kuma a watan Afrilun shekarar bara ta kori wasu jam'an Rasha hudu bayan bankado kisan da aka yi wa mutane da dama a Boutcha, dake wajen birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine.