Osinbajo ya jaddada alkawarin kawar da Boko Haram | Siyasa | DW | 21.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Osinbajo ya jaddada alkawarin kawar da Boko Haram

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kawo wata ziyarar aiki Jihar Borno inda ya tattauna da shugabannin jihar kan matakan shawo kan matsalar tsaro a sakamakon zafafar hare-haren Boko Haram.

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya kawo wata ziyarar aiki Jihar Borno yau inda ya gana da shugabannin jihar da kuma masu ruwa da tsaki kan harakokin tsaro kan matakan tunkarar kara tabarbarewar tsaro a shiyyar Arewa maso gabashin Najeiya saboda zafafa hare-haren da mayakan Boko Haram su ka yi a ‘yan kwanakin nan.

A ‘yan kwanakin nan dai mayakan na Boko Haram sun kai jerin hare-haren a sassan jihohin Borno da Yobe inda su ka hallaka matane da dama ciki har da jami’an tsaro na soji da faren hula abin da ake ganin mai da hannun agogo baya ne a yaki da Boko Haram.

Wadannan hare-hare sun kai ga a makon da ya wuce gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bakin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yomi Osinbajo ayyana cewa mayakan Boko Haram na ci gaba da mamaye wasu yankunan a jihar Borno.

Bisa wannan ne mataimakin shugaban Najeriyar ya kawo wata ziyara yau a Maiduguri domin nuna damuwa kan halin da ake ciki da kuma saduwa da masu ruwa da tsaki don tattaunawa kan yadda za a samo bakin zaren magance koma-bayan tsaro da ake samu a wannan lokaci.

Nigeria Kashim Shettima, Gouverneur Borno (Reuters/A. Sotunde)

Kashim Shettima gwamnan Jihar Borno a Najeriya

Farfesa Osinbajo mataimakin shugaban Najeriyar ya zaga inda ya gana da a al’umma da kuma jami’an gwamnati tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi dukkanin mai yiwuwa don magance wannan matsalar tsaron da sake gina shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya kamar dai yadda ya tabbatar wa shehun Barno a fadarsa a lokacin da ya kai ziyara inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

" Dangane da damuwa da ake nunawa kan sake gina shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya shi ne babban kalubale da ke gaban gwamnatinmu. Ina kuma kara ba ku tabbacin cewa wannan shi ne ma muka sa gaba a matsayin na gwamnatin tarayya. Ba a jima ba shugaban kasa ya rattaba hannu kan dokar kafa hukumar raya shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya abin da ke nuna cewa mun samu madogara ta sake farfado da shiyar”

Daga nashi bangare Gwamnan Jihar Borno Kashim Shetima ya bayyana cewa duk da matsalolin na tsaro da yankin ya fada ba za su daina fatan fita daga cikin wannan matsala musamman da irin mai da hankali daga gwamnatin tarayya inda ya yi karin bayani yana mai cewa:

" Mun shiga mawuyacin hali a shekaru da lokuta da suka gabata amma wannan ba zai sa mu cire fatan fita daga duk wani kangi da muka samu kanmu a ciki ba. Kamar yadda Mathew Lutha King yake fada ba a gane mazantaka mutum daga yanayin jin dadin da ya samu kansa a ciki sai dai irin juriyarsa a lokacin da ya samu kansa a lokacin kalubale da rigingimu”

Dukkanin masu ruwa da tsaki sun yi wa mataimakin shugaban kasar jawabi da kuma gabatar da rokon al’ummominsu. Shehun Borno Alh ABubakar Inb Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya yi roko ga gwamnatin tarayyar kamar haka.

“Ya ina mika kokon bara gare ku, mayakan Boko Haram sun kashe mana ‘ya ‘yanmu maza da mata. Muna fata gwamnati za ta dube mu da idon basira a dauki ‘ya ‘yanmu aiki a ba su mukamai a gwamnati kuma muka roko ba mu kulawa ta musamma".

Al’ummar Maiduguri sun yi fatan wannan ziyara ta mataimakin shugaban kasa za ta haifar da daukar matakai na magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar. Kafin ya koma Abuja sai da mataimakin shugaban ya ziyarci wata makaranta da ya gina domin marayu da kuma kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar Borno ta gudanar.

Sauti da bidiyo akan labarin