1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Omicron zai janyo tsaiko a wasannin Olympics

Binta Aliyu Zurmi
November 30, 2021

Sabon nau'in corona na Omicron na neman zama barazana ga wasannin Olympics da ke tafe a birnin Beijing na kasar China a shekarar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/43fIh
China Peking | Olympische Winterspiele 2022 | Übergabe des Olympischen Feuers
Hoto: NOEL CELIS/AFP/Getty Images

Mahukunta a Beijing sun yi gargadin cewar sabon nau'in corona na Omicron da ke saurin yaduwa a cikin al'umma zai janyo kalubale a wasannin Olympics na lokacin sanyin hunturu da za a gudanar a watan Fabarairun shekarar 2022.

Da yake jawabi a game da bullar sabon nau'in na corona, mai magana da yawun ma'aikatar wajen kasar Chinar Zhao Lijian ya bayyana cewar za a fuskanci kalubale, amma kasancewar kasar ta sha fama da wannan cutar wacce suka yi nasarar dakile a, za su yi duk mai yiwuwa na ganin wassannin ya kankama ba tare da fargabar baza cutar ba.

Dubban 'yan wasa da 'yan jarida gami da wadanda za su halarci wasan daga wasu kasashen duniya za a kebe su har na wani lokaci kafin gudanar da wasannin.