Obama ya gana da shugabannin yankin Gulf | Labarai | DW | 21.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya gana da shugabannin yankin Gulf

Barack Obama ya halarci taron kolin majalisar hadin kan kasashen yankin Gulf a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

A wannan Alhamis Shugaban Amirka Barack Obama ya gana da manyan jami'an kasashen Larabawa shida inda suka tattauna kan batutuwan tsaro a yankin tekun Pasha da kuma yaki da kungiyar IS mai da'awar kafa Daular Musulunci a Iraki da Siriya. Obama ya gana da shugabannin kasashen Saudiyya da Kuwaiti da Qatar da Bahrain da Oman da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa a birnin Riyadh. A taron inda kuma aka tabo maganar samar da kwanciyar hankali a yankin da rage zaman dar-dar tsakanin kasashen Larabawa da Iran, ya zo ne bayan makamancinsa da aka gudanar bara a Camp David da ke a Maryland. Kasashen Larabawa na nuna rashin jin dadinsu da irin kusancin da ake samu yanzu tsakanin Amirka da Iran.