Obama da Putin za su gana kan rikicin Siriya | Labarai | DW | 24.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama da Putin za su gana kan rikicin Siriya

Shugaban Amirka Barack Obama da takwaransa na Rasha Vladmir Putin za su yi wata tattaunawa a birnin New York na Amirka ranar Litinin din da ke tafe.

Mai magana da yawun Shugaba Putin Dmitry Peskov ya ce shugabannin biyu sun amince su yi ganawar ce don radin kansu duk kuwa da cewar Moscow da Washington na zaman doya da manja sanadiyyar rikicin da ake yi a gabashin Ukraine.

Ganawar Obama da Putin dai za ta maida hankali ne kan yakin basasar da kasar Siriya ke fuskanta da kuma hanyoyin da za a bi wajen kawo karshensa sannan kakakin Putin din ya ce in hali ya yi shugabanni biyu za su tattauna kan rikicin Ukraine.