NNPC: Ba za mu yi karin kudin mai ba | Labarai | DW | 05.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

NNPC: Ba za mu yi karin kudin mai ba

Kamfanin mai mallakin gwamnatin Najeriya NNPC ya ce jita-jitar da ake yadawa kan karin kudin mai a kasar ba ta da wani tushe balle makama.

Wata sanarwa da shugaban kamfanin Dakta Maikanti Baru ya fidda na cewar kamfanin bai da wata niya ta karin kudin man fetur da dangoginsa sannan ya na da isasshen mai da zai wadaci al'ummar kasar don haka su kauracewa rubibi wajen sanyen man don gudun dagulewar lamura. Tuni ma dai Dakta Baru ya bayyana katse wata ziyara da ya ke Burtaniya domin shigewa gaba wajen daidaita al'amura inda yanzu haka ya ce ya bada umarnin tunkuda karin man fetur zuwa sassan kasar daban-daban don kawo karshen halin da ake ciki.