1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar:An gudanar da bikin a'aldu na makiyaya

Tila Amadou AH
September 19, 2017

Mako guda aka kwashe tun daga ranar 15 har zuwa 16 ga watan Satumba ana gudanar da bikin makiyayan da ake yi wa la'akabi da Cure Salée ko kuma lasar gishiri a garin Ingall da ke cikin Jihar Agadez a arewacin Nijar.

https://p.dw.com/p/2kFpu
Niger The Cure Salée Nomaden-Festival
Hoto: DW/T.Amadou

Bikin Cure Salée dai ko kuma lasa gishiri biki ne da ke hada makiyaya Nijar baki daya, kuma wannan shi ne karo na 54 da ake gudanar da bikin a karkashin jagoranci firaministan Nijar Birji Rafini. Makiyayan dai kan yin amfani da wannan dama domin nuna al'adunsu tun daga tufafi, kitso, kafin a yi gasar fitar da sarauniyar kyau da kuma naminji da ya fi kowa kyau a tsakanin makiyayan. Kuma a bana ma an gudanar da bikin ne kamar yadda aka saba a kowace shekara lami lafiya.