1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar za ta biya diyya ga yaran da ruwa ya nakasa

Ramatu Garba Baba
October 22, 2018

Gwamnatin jamhuriya Nijar ta shirya biyan iyalan yaran da suka samu nakasa diyya na Yuro miliyan uku a sanadiyar shan ruwan da ya gurbace daga yawan sinadarin Flouride.

https://p.dw.com/p/36vPA
Nigeria Polio Virus
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Sanarwar ta kafar talabijin a kasar ta ce akalla yuro miliyan uku za a biya wadanda lamarin ya shafa. Ministan kudin kasar Hassoumi Massoudou a jawabinsa ga 'yan majalisar kasar, ya ce babu dalilin da gwamnati ba za ta biya diyyan ba tun da kotu ta bayar da umarnin yin hakan, sai dai ministan bai fadi lokacin da za a soma biyan kudin ba.

A shekarar 2000 ne, likitoci suka lura da yawan yara 'yan shekara tsakanin daya zuwa goma sha biyar da suka samu nakasa a kusan lokaci guda a yankin Tibiri, daga baya ne bincike ya gano ruwan da jama'a suka yi ta anfani da shi mai cike da sinadarin Floride da ya wuce kima ne musabbabin matsalar, da ta haifar da cutar nakasa ga yara sama da dubu hudu da dari tara.