1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Za a yi wa kundin zaben gyaran fuska.

Abdoulaye Mamane Amadou
September 27, 2018

Majalisar tattauna al’amurran siyasar Nijar CNDP ta ware ranar 1 ga watan Oktoba domin daukacin Jam’iyyun siyasar kasar su hadu don yin mahawar game da sake tsarin kundin zabe.

https://p.dw.com/p/35bTD
Mahamadou Issoufou Präsidentschaftskandidat Niger
Shugaban Nijar Muhammadou IssoufouHoto: DW

Bayan bore da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Jam’iyyun siyasar kasar na ‘yan adawa da bangaren masu rinjaye majalisar tattauna al’amurran siyasar kasar CNDP ta ware ranar 1 ga watan Oktoba domin daukacin Jam’iyyun siyasar kasar su hadu don yin mahawar game da batun sake tsarin kundin zaben.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Firaministan kasar Brigi Rafini, gwamnatin ta Jamhuriyar Nijar ta gayyaci ‘yan adawa da daukacin jam’iyyun siyasar kasar da su hau kan teburi guda na shawara domin samun daidaito game da batun kudin tsarin zaben kasar (code electrol) a karkashin jagorancin majalisar tattauan al’amurran siyasar Nijar CNDP.

Ba tun yau ba dai ake ta kai ruwa rana tsakanin bangarorin jam’iyyun siyasar kasar game da batun na kudin tsarin zaben wanda a can baya gwamnatin da ma jam’iyyun da ke bangaren masu mulki suka kekasa kasa na kin jin koken ‘yan adawar da ma sauran jam’iyyun da ke rakiyar gwamnatin ta ‘yan renaissance.

Malam Annabo Samaila shugaban Jam’iyyar Mdnd Kokari kuma kakakin kawancen ‘yan adawa na FRDDR yace ba haka kawai suka ce a sake tattaunawa ba. Tun farko bangaren gwamnati ya nuna kin amincewa.

‘Yan adawar dai sun shafe tsawon shekara daya suna kauracewa taron hukumar tattauna al’amurran siyasa ta kasa CNDP da ma kin shiga a dama da su a hukumar zabe mai zaman kanta CENI bisa wasu korafe-korafe ciki har da kundin tsarin zaben da suka jima da haramtawa lamarin kuma da yakai ga wasu jam’iyyun da ke marawa gwamnati baya irinsu Mpn kishinkasa ta Ibrahim Yacouba ficewa daga kawancen masu mulki.

Sai dai a yanzu ga alama sun ce suna cikin shawara domin karbar kiran gwamnati da zummar samun mafita.