1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu juna biyu sun fi kamuwa da cutar HIV a Nijar

November 30, 2018

Alkaluma sun nuna yadda mata masu juna biyu suka kasance a sahun gaba daga cikin wadanda suka kamu da cutar HIV ko SIDA a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/39DlX
Kaiserschnittgeburt in Niamey im Niger
Hoto: Imago/S. Backhaus

A yayin da ake tuni  da zagayowar ranar 1 ga watan Disamba da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da cutar HIV ko SIDA, an gano yadda masu juna biyu sune suka fi kamuwa da cutar fiye da sauran al'umar kasa. Alkalumman mizanin gwajin cutar ne ya nunar da hakan abin da ya kuma haifar da fargaba da kuma mayar da hannun agogo baya a yaki da ake da wannan annoba.


''Kowa ya san matsayinsa'' shi ne taken taron na bana, to sai dai a yankin Damagaram na Jamhuriyar ta Nijar da ke gaba gaba a jerin yankunan kasar da ake ganin girman cutar, alkalumman kungiyoyin yaki da cutar sun  bayana cewar daga shekarar 2015 zuwa 2016 a jimilce, mutane dubu tamanin da tara da dari biyu da tamanin da tara ne suka yi gwaji, sannan daga cikin mata masu juna biyu akalla dubu tamanin da uku da dari hudu da talatin da suka yi gwajin cutar, dubu daya da dari shida da sittin ne kadai suka amince da yin gwajin cutar a radin kan su. Lamarin da ke haifar da tarnaki a kokarin da ake na son sanin alkaluma na masu fama da cutar. Game da wannan matsala ya sa a baya bayan nan  gwamnatin Nijar a yayin wani zama da majalisar ministoci, ta dauki matakin kawar da cutar kafin nan da shekara ta 2030.