Nijar: Yaki da yaduwar cutar SIDA a Jihar Tahoua | Zamantakewa | DW | 20.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Nijar: Yaki da yaduwar cutar SIDA a Jihar Tahoua

Jami'an kiyon lafiya da ma sauran kungiyoyin yaki da SIDA ko AIDS na cigaba da kokarin fadakar da al'umma, don taikata yaduwar cutar.

Ebola in Sierra Leone überwunden

Binciken lafiya domin sanin matsayin mutun game da cutar Sida

Cutar Sida ko kuma AIDS mai karya garkuwar jikin dan Adam, na daga cikin cututukan da suka lakume rayukan dubban jama'a a Jamhuriyar Nijer a shekarun da suka shude. To sai dai a halin yanzu, himmar da aka sa a game da yaki da wannan cuta, ta taimaka sosai ga samun ragowar masu kamuwa da ita musamman a yankunan kasar irin su jihar Tahoua, inda ake samun 'yan ci-rani da masu fatauci da kasashen waje masu yawan gaske. A cewar Usman Ag Abdoulahi shugaban cibiyar kula da yaki da cutar ta SIDA ta Jihar Tahoua an samu ci-gaba sosai a wannan yaki:

Blutabnahme für HIV-Test in Südafrika

Likita na daukan jini domin gwaji

"Da farko dai bincike ya nunar cewa, cikin mutun 100 ana samun mutun daya mai dauke da kwayar cutar ta SIDA. Sannan kuma wani bicike da aka yi ga musali a nan jihar Tahoua ga mata masu zaman kansu cikin 100 ana samu 30 masu dauke da cutar da sida amma kuma daga bisani bincike ya nunar cewa an samu babbar ragowa."

A kowace shekara dai, dubban majiya karfi ne ke barin jihar ta Tahoua domin zuwa yawon bida a wasu kasashen waje, sannan 'yan kasuwa masu fataucin albasa da ke zaman babban abun da ake kasuwanci da shi a jihar ta Tahoua, ke zuwa da zowa a wasu kasashen ketare, da kuma drebobi masu manyan motoci inda ake zargin wasun su na shigowa da cutar. Sai dai a cewar Sumaila Mahamadou Sakataran kungiyar masu manyan motoci hakan ta sanya an dauki manyan matakai na kaucewa kamuwa ko yada cutar ta SIDA tsakanin al'umma:

Antiretrovirale Medikamente HIV AIDS Mosambik Afrika

Magungunnan rage karfin cutar SIDA

" Lalle ne an yi ayyukan wayar da kan jama'a kan wannan batu. An kirayi drebobi masu suhuri, da sauran jama'a masu yawan zuwa kasashen waje. Sannan kuma aka je wurare kamar inda jami'an tsaro masu bincike ke tsayawa na bakin hanya domin wayar da kanun drebobi masu ficewa."

Kungiyoyi daban-daban dai sun taka rawar gani a yakin da ake da cutar, inda masu kula da fadakar da mata masu zaman kansu suma suka yaba irin cigaban da aka samu wajen takaitar yaduwar cutar da ma daukan cikin da ba a shirya mishi ba. Suma dai daga nasu bangare kafofin yada labarai sun taka rawar gani a fannin fadakarwa domin akasarin kungiyoyin na bin ta kansu ne domin isar da sakonni ga al'umma ta yadda za su tsare kansu.