Nijar: Tururuwar ′yan gudun hijira daga Najeriya | Labarai | DW | 08.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: Tururuwar 'yan gudun hijira daga Najeriya

Hare-haren kungiyar Boko na ci gaba da tilasta wa 'yan gudun hijira daga Najeriya shiga Jamhuriyar Nijar don samun mafaka inda a yanzu suke fakewa a iyakar kasar da kuma kasashen makwabtan Nijar din.

Akalla 'yan gudun hijra dubu 100 suka kaurace wa gidajensu domin samun mafaka a wasu yankunan kasar Jamhuriyar Nijar sakamakon karuwar tsanantar hare-haren mayakan Boko Haram a wasu sassan Najeriya. 

Kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP ya ruwaito Fatouma Bintou Djibo babbar jami'ar hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya na cewa, tsanantar hare-haren da mayakan suke ci gaba da yi a kwanakin nan ya haddasa wani hali na tasko ga al'umma.  

Ko baya ga yankin na Diffa da ke karbar sababbin 'yan gudun hijirar, yanzu hakan da akwai wasu 'yan gudun hijira fiye da dubu 20 000 a yankunan kasar ta Nijar masu makwaftaka da Zamfara, biyo bayan 'yan bindiga sun yiwa garurwansu yankan kauna, kana kuma wasu fiye da dubu 70 000 ke samun mafaka daga kasashen Mali da Burkina Faso, lamarin da wata sanarwa hukumar ta ce dole ne sai an taimaka.