1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar sojin Nijar sun nada firaminista

Abdoulaye Mamane Amadou Abdourahmane Hassane
August 8, 2023

Gwamnatin mulkin sojin da ta yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ta nada Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin sabon firaministan gwamnatin rikon kwarya

https://p.dw.com/p/4Ut68
Niger | General Tchiani übernimmt Macht nach Putsch gegen Präsident Bazoum
Janar Abdourahmane Tchiani jagoran juyin mulkin Jamhuriyar NijarHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

An nada Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin sabon fraministan gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Nijar. A cikin wata sanarwar da kakakin sojin da suka aiwatar da juyin mulkin Nijar din ya karanto a kafar talabijin a yammacin jiya aka sanar da nadin. Kafin wannan lokaci Ali Mahaman Lamine Zeine ya rike mukamin ministan kudi da tattalin arzikin Nijar a yayin gwamnatin Tandja Mamadou, kafin nada shi a mukamin wakilin bankin raya kasashen Afirka BAD a kasashen Côte d'Ivoire da Gabon da kuma kasar Chadi.Ko baya ga nadin sabon firaministan wmajalisar sojin da suka kifar da gwamnati, sun kuma yi wasu karin nade-nade cikli har da na babban kwamadan rundunar da ke gadin fadar shugaban kasa.