Nijar ta yi karin bayani kan yinkurin juyin mulki | Labarai | DW | 19.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar ta yi karin bayani kan yinkurin juyin mulki

Lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Asabar minstan cikin gida na Nijar ya tabbatar da kame sojoji tara tare da bayyana sunayen wasu daga ciki.

Ministan cikin gida na kasar Jamhuriyar Nijar Hassoumi Masaoudou ya bayar da karin haske dangane da batun bankado yinkurin juyin mulkin da gwamnatin kasar ke zargin wasu manyan sojojin kasar da yi a cikin wannan mako.

Lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Asabar ministan ya tabbatar da kame wasu manyan sojoji tara da suka hada Janar Suleimane Salou tsohon hafsan sojin kasar ta Nijar da Kanal Abdou Dan Haoua komandan na rundunar soji tsaron filin jirgin sama na birnin Yamai da komandan Nare Maidoka shugaban bataliyar sojojin masu sarrafa manyan makamai ta daya da ke a birnin Tillabery na Yammacin kasar.

Akwai kuma Issoufou Oumarou Komandan na rundunar musamman ta yaki da ta'addanci da ke da cibiya a fadar shugaban kasa, da Kaptain Amadou Chekaraou shi ma na rundunar sojin masu yaki da ta'addanci da ke arewacin birnin Yamai.

Ministan ya kuma ce akwai wani laptana da ya tsere da farko kafin ya dawo ya mika kansa ga hukumomin tsaro.

Ministan ya ce wasu daga cikin sojojin da aka kitsa shirin da su ne suka tona asiri. Sannan ya ce suna da isassun hujjoji da suka hada da sakonnin SMS dama wasiku da sojojin da suke zargin suka dinga masanya a tsakanin su.

Sai dai ministan ya ce kawo yanzu dai babu wani farar hula da aka samu da hannu a cikin lamarin wanda ya ce tuni aka mika aikin bincike ga hannun hukumar Jami'an tsaron Jandarma ta kasa.