1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiAfirka

Nijar ta kayyade kudade da ayyukan kananan hukumomi

Salissou Boukari Mouhamadou Awal
March 6, 2026

Manyan jami'an Nijar sun yi nazarin hanyoyin samar da kudaden shiga ga kananan hukumomi da nufin kashe su don kyautata rayuwar al’umma. Sai dai ana samu magabatan da ke neman azirta kansu maimakon yi wa al'umma aiki.

https://p.dw.com/p/59wF8
Banknoten CFA Francs 2004
Hoto: Seyllou/AFP

Ma'aikata kwararru na ma'aikatar cikin gida da shugabannin kananan hukumomi da masu ajiyar kudade da sarakunan gargajiya sun yi musayar dubaru kan hanyoyin samar da kudaden shiga ga kananan hukumomi domin saka su a mahimman ayyukan ci-gaba, ta yadda al'umma za su gani karara a kasa, ba wai bisa takardu kawai ba.

Abdoul Kadri Hama Assa, babban Darekta a ma'aikatar kula da kananan hukumomi na Jamhuriyar Nijar ya ce: "Shugabannin kananan hukumomi su yi la'akari da cewa kudade ne da za a yi aiki da su don gina kasa, ba kudade ba ne da ake abin da aka ga dama da su ba." Ya kara da cewa " dole daga lokaci zuwa lokaci, kananan hukumomi su yi wa al'umma bayani kan abin da aka tanada, da abin da ake da niyyar yi, da wanda aka yi. Wannan shi ne ke kawo yarda tsakanin talakawa da shugabannin kananan hukumomi."

Bambanci tsakanin siyasa da mulkin soji

Ana zagin Bazoum da Issoufou da kawar da kai kan barnatar da kudin kananan hukumoni
Ana zagin Bazoum da Issoufou da kawar da kai kan barnatar da kudin kananan hukumoniHoto: Aboubacar Magagi

A lokacin 'yan siyasa a karkashin tsari na dimukuradiyya, shugabannin kananan hukumomi sun ta yin sharholiya da kudaden jama'a, inda wasu ma suka kare a gidan kaso, wasu kuma aka kawar da kai a kan barnar da suka tafka. Ko a yanzu, wasu shugabannin kananan hukumomin na tunanin cewa an basu wannan mukami ne don su azirta kansu ko kuma su yi gyaran ritayarsu maimakon aiki na fita kunya ga kasa.

Amma Dokta Atto Namaiwa, mai sharhi kan harkokin shari'a, ya ce yana da kyau gwamnati ta dauki kwararan matakai na kare arzikin kananan hukumomi. Ya ce: " Al'umma sun samu damar sa ido a kan yadda ake jagorancin kananan hukumomi, kuma su samu damar sanin manufar wannan aiki, la'akari da yadda barna ta yi katutu a zukatan wadanda aka rataya wa nauyin jagorancin kananan hukumomi."

Sai dai Ousmane Alasmagui, shugaban karamar hukumar Aderbisnat a cikin jihar Agadez ya ce akwai magabaci da ya yi abin da ya ga dama da dukiyar al'umma: Ya ce: " Yanzu wannan mulki ba a karkace yake ba, duk wanda ya karkata ya kawo ma kansa jidali."

Tiani: "Ba sani ba sabo"

Janar Tiani ya yi barazanar ladabtar da duk wanda za a samu da karkatar da dukiyar kasa
Janar Tiani ya yi barazanar ladabtar da duk wanda za a samu da karkatar da dukiyar kasaHoto: Boureima Hama/AFP

A wata tattaunawa da aka yi da shi, shugaban mulkin sojin Nijar Jana Abdourahamane Tiani, ya sanar cewa duk wanda aka ba wa mukami, za a sauke shi idan ya kauce hanya kamar yadda aka gani ga kananan hukumomi da ma gundumomi da dama. Amma har yanzu da dama daga cikin 'yan Nijar na ganin cewa matakin ba sani ba sabo ya kamata ya shafi kowa domin ba wa gawa kashi don mai rai ya ji tsoro.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani