Nijar ta karbi maganin Covid 19 daga Madagaska | Labarai | DW | 05.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar ta karbi maganin Covid 19 daga Madagaska

Gwamnatin Nijar ta karbi a wannan Talata tallafi maganin cutar Corona daga gwamnatin kasar Madagaska, kasar da ta samar da kanta maganin da ta yi wa suna Covid-Organics.

Gwamnatin Nijar ta karbi a wannan Talata maganin cutar Corona na gargajiya wanda gwamnatin kasar Madagaska ta tallafa Nijar din da shi kyauta ruwan Allah, domin yakar cutar ta Covid 19 a kasar ta Nijar

 Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito Ismagail Annar daraktan ofishin ministan kiwon lafiya na cewa za su yi amfani da maganin ne mai suna Covid-Organics wanda kasar madagaska din ce ta samar da shi da kanta, a kan mutane 900, wato 300 daga cikin wadanda ke dauke da kwayoyin cutar da kuma kan wasu mutanen 600 a matsayin rigakafi.

 Nijar dai na a matsayin kasa ta uku bayan Guinea Bissau da kuma Equatorial Guinea da ta samu tallafin maganin na Covid Organics daga kasar ta Madagaska. Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce babu wani gwajin kimiyya da aka gudanar a kan ingancin wannan magani. 

Alkalumman gwamnatin kasar ta Nijar na farkon wannan mako sun nunar da cewa cutar ta Corona ta harbi mutun 755 a kasar ta kuma kashe 37 da suka hada da tsohon ministan kwadagon kasar Malam Ben Omar Mohamed wnda Allah ya yi wa rassuwa a ranar Lahadin da ta gabata.