Nijar ta kafa dokar haramta fataucin jakai | Zamantakewa | DW | 09.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Nijar ta kafa dokar haramta fataucin jakai

Gwamnatin Nijar ta kafa dokar haramta fataucin jakai a wani mataki na kare jakan daga barazanar karewa, ganin yadda fataucin jakunan zuwa kasashen Asiya ya habbaka a shekarun baya-bayan nan.

Wani kudirin doka ne wanda ya hada ma'aikatun gwamnatin kasar ta Nijar hudu da suka hada da ta ministan kiwo da na cikin gida da na kasuwanci da kuma na kudi, ya tanadi matakin harmcin fataucin jakunan ko namansu ko kuma fatunsu zuwa kasashen ketare. Ko baya ga barazanar yanayi na fari jakunan na fuskantar barazanar bacewa ne a sakamakon yadda ake fataucinsu daga Nijar zuwa Najeriya, inda daga nan ne bayan an yi amfani da namansu ake fataucin fatunsu zuwa kaashen Asiya musamman kasar Chaina.

Wasu alkalumman kididdiga na kasar ta Nijar sun nunar da cewa kasar ta mallaki jakuna miliyan daya da rabi. Sai dai kuma wasu alkalumman hukumar kwastam ta kasar ta Nijar sun nunar da cewa adadin yawan jakunan da aka fice da su daga Nijar ya tashi daga jakuna dubu 27 a shekara ta 2015 zuwa sama da dubu 80 a cikin watanni biyar kawai na farkon wannan shekara ta 2016 da muke ciki. Wani dillalin jakuna a wata kasuwar jakunan garin Mangaize na yammacin kasar ta Nijar ya bayyana cewa budewar wannan kasuwa ta jakunan ta haddasa tashin farashinsu a kasuwannin kasar inda kudin jaki daya ya tashi daga jaka 40 na cefa wato kwatankwacin euro 61 zuwa jaka dari na cefa wato kwatankwacin euro 152.

Sai dai tuni farashi kudin jakin ya soma faduwa a kasuwannin kasar ta Nijar tun bayan da kasar ta dauki wannan doka ta haramta fataucinsu. A watan Agustan da ya gabata ma dai kasar Burkina Faso mai makwabtaka da kasar ta Nijar ta dauki irin wannan mataki na haramta fataucin jakunan zuwa kasashen ketare, a wani yunkuri na kare nau'in wannan dabba daga barazanar karewa a cikin kasar, inda jama'a da dama ke amfani da su a matsayin abin hawa da ayyukan gona da na yau da kullum.