Nijar ta dawo da intanet | Labarai | DW | 06.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar ta dawo da intanet

Wakilin DW a Damagaram Larwana Malam Hami ya ce a daren Jumma’a wayewar garin Asabar ne ‘yan Nijar suka fahimci cewa intanet ta dawo a kasar bayan kwanaki goma da hukumomi suka toshe shiga shafukan sada zumunta.

Rahotannin da ke fitowa daga sassa daban-daban na Jamhuriyar Nijar na nuna cewa hukumomi sun saki intanet bayan kwashe kwanaki da takaita amfani da ita. Jim kadan ne dai bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da ya nuna cewa dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazoum Mohamed ne ya lashe zaben, sai matasa suka fantsama kan tituna da shafukan sada zumunta suna nuna rashin amincewarsu, suna zargin an tabka magudi.

Daga nan sai kwatsam aka wayi gari an toshe shiga intanet din a kasar, abin da ya sa wasu fassara matakin da cewa hukumomi sun yi haka ne domin dakile rikicin bayan zabe.

Abdu Bagobiri na cikin 'yan Nijar a Damagaram da suka yi marabá da dawo da intanet din. Ya ce tsaikon da aka samu ya sanya jinkiri a wurin isowar wasu kudade da aka turo masa daga Najeriya.